16 Agusta 2021 - 15:19
Afghanistan: An Yi Kashe-kashe Yayin Rudanin Da Ya Barke A Filin Jirgin Saman Kabul

Rahotanni daga Afghanistan na cewa an fuskanci rudani a filin jirgin saman Kabul wanda ya kasance wani tudun mun tsira ga ‘yan kasashe waje da kuma ‘yan Afghanistan sa’o’i kadan bayan da ‘yan Taliban suka karbe mulkin kasar.

ABNA24 : Wasu rahotannin sun ambato cewa sojojin Amurka sun bude wuta yayin da 'yan Afganistan ke kokarin shiga jiragen saman da ake korarin kwashe ‘yan waje.

Wasu bayanai na daban sun ce an samu mace mace yayin bude wutar da sojojin na Amurka sukayi koda wasu sun ce harbin sama ne akayi.

Amma kamfanin dilancin labaren Reuters ya ce mutane da dama sun mutu yayin rudanin.

342/